Fada tsakanin Sojen Najeriya da ′yan bindiga. | Labarai | DW | 26.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada tsakanin Sojen Najeriya da 'yan bindiga.

A wani kokari na kwato 'yan mata 'yan makaranta da aka sace a Najeriya, sojojin kasar sun fafata da masu kai harin a yankin Bulanbuli na jihar Borno.

Rahotanni daga Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya sun ce an gwabza wani kazamin fada a daren jiya Juma'a (25.04.2014) a kusa da wurin da ake tsammannin nan ne ake rike da daruruwan 'yan matan nan 'yan makaranta da wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka sacesu.

Fadan da ya wakana a wajejen garin Bulanbuli dake cikin jihar Borno, ya yi sanadiyar mutuwar maharen akalla guda 40, yayin daga bangaren dakarun gwamnati sojoji hudu suka mutu wasu kuma tara suka jikata, a cewar kakakin tsaron kasar ta Nageriya Janar Chris Olukolade.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labarin. Amma kuma wasu mazamna garin Chibok inda aka sace 'yan makarantar sun ce sun ji karan manyan makammai dake fitowa daga dajin na sambisa. A satin da ya gabata ma dai anyi ta samun labarai masu karo da juna kan wannan batu.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe