Fada tsakanin manoma da makiyaya a Chadi | Siyasa | DW | 24.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fada tsakanin manoma da makiyaya a Chadi

Kasar Chadi na cikin kasashen yankin Sahel da ke fuskantar rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da ke dada karuwa tare da  sanadiyyar rasa rayukan mutane da yawa.  

Ana zargin wasu shugabannin kananan hukumomin da tallafa wa makiyaya a wannan rikici, lamarin da ya sa yawancin 'yan Chadi suka nemi gwamnati ta tsawata don a samar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya. Mayo Kebbi da Tandjilé da ke a gabashin kasar sun yi fama da rikice-rikice da dama tsakanin makiyaya da kuma manoma da ke zama 'yan asalin yankunan. Akalla mutane sittin ne suka mutu a cikin wadannan rikice-rikicen da suka ki ci suka ki cinyewa. Ba komai ba ne ya haddasa su ba, illa lalata gonakin manoma da dabbobin makiyaya ke yi. Hasali ma a duk lokacin da manoma suka nemi kare gonakin su, galibin su na martani daga makiyaya wadanda ke yin amfani da makamai wajen far wa manoma. Sai dai wani abu guda na dada rura wutar rikicin, wato daurin gindi da makiyaya ke samu daga wasu shugabannin yankunan da rikice-rikicen suka shafa.

An bukaci Shugaba Idriss Deby Itno da ya tsawata a kan rikicin manoma da makiyayan a Chadi

Halin da ake ciki a Chadin ya sa bishof-bishof na kasar a cikin sakon su na Kirsimeti, sun gayyaci shugaban kasar Idriss Deby Itno da ya sauke nauyin da ke kan sa na kare rayuka 'yan kasar ciki har da manoma. Abbot Xavier shi ne sakataren kungiyar Bishop-bishop na Chadi. “Muna yin kira ga shugaban kasa da ya hanzarta yunkurawa don kawo karshen wadannan rikice-rikicen da suka dade suna faruwa, wadanda suka haifar da zaman kara zube a Chadi. Mun ga cewa mutane da dama sun mutu, mun ga wadanda suka sami raunuka a cibiyoyin kiwon lafiya. Wadannan rikice-rikicen sun yi barna sosai a matakan tattalin arziki, zamantakewa da na rayukan mutane. Don haka ya kamata shugaban kasa ya sake duba wannan matsalar, wacce ke haddasa mace-macen iyalai fiye da sauran rikice-rikicen. Ko da ita Hukumar kare hakkin dan-Adam ta kasar Chato (CNDH) a takaice sai da ta mika wannan bukata ga gwamnati ta magance rikicin manoma da makiyaya cikin hanzari. 

Sauti da bidiyo akan labarin