Fada ta barke a Guinee | Labarai | DW | 15.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada ta barke a Guinee

Soojoji sun tarwatsa wasu mata da ke kokarin tayar da fitina a Conakry babban birnin kasar Guinee

default

Matasa masu zanga zanga a Guinea

An bada rahoton cewa fada ta barke tsakanin jam'ian tsaro da da wasu daruruwan matasa a Conakry Babban birnin kasar Guinee, a dadai lokacin da ake cikin zaman jiran hukumar zabe ta kasar ta bayyana sakamakon zaben  na shugaban kasar da aka gudanar a makon jiya.

Wani babban jam'in yan sanda da ya ce sun tarwatsa matasan galibi magoya bayan tsohon Firaminista Cellou Dalein Diallo,

ya ce suna kokarin tayar da fitinan ne a wata cibiyar ta yan siyasar a sa'ilin da suka fatatakesu.Nan da wani lokaci ne dai a yau aka shirya hukumar zaben za ta bayyana dan taraka da yayi nasara a zaben shugaban kasar zagaye na biyu tsakanin Alpha Conde da Mista Diallo.

Mawallafi : Abdurahamane Hassane

Edita        : Abdullahi Tanko Bala