Faɗa na ƙara yin muni a Gaza | Labarai | DW | 01.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faɗa na ƙara yin muni a Gaza

Amirka da Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi Allah wadai da karya yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cimma tsakanin Hamas da Isra'ila.

Sakataran harkokin wajen Amirka John Kerry ya zargi Hamas da kasancewar sanadiyyar wargajewar yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cimma ta sao'i 72. A cikin wata sanarwa da ya bayyana Kerry ya buƙaci Hamas da ta sako wani sojin Isra'ila da aka rawaito cewar ya ɓace wanda kuma Hamas ke yin garkuwa da shi.

Sakataran harkokin wajen na Amirka ya kuma yi kira ga ƙasashen duniya da su matsa ƙaimi wajen ganin cewar sun dakatar da hare-haren rokoki ta hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da Hamas ke kai ma Isra'ila. Shi ma babban sakataran Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya ce ya zama wajibi Hamas ta gaggauta sako sojin ba tare da gindaya wasu sharuɗa ba.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu