EU za ta yi waiwaye kan rikicin Rasha da Ukraine | Labarai | DW | 29.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta yi waiwaye kan rikicin Rasha da Ukraine

Ministoshin harkokin wajen Tarayyar Turai za su duba jerin takunkumin karya tattalin arziki da suka aza wa Rasha bisa zargin ta da hannu a rikicin gabashin kasar Ukraine

A yau Alhamis ne ministocin harkokin wajen za su yi taron nasu. Yanzu haka dai fada tsakanin yan aware da Rasha ke marawa baya da gwamnatin Kiev wanda ke dasawa da kasashen Yamma, yakaru matuka fiye da gabanin sa hannu bisa yarjejeniyar tsakaita wuta da aka yi. Tuni dai jerin takunkumin dama wasu matakan karya tattalin arziki da kasashen Yamma suka dauka kan Rasha, suka fara yin tasiri. Inda a jiya Laraba ministan harkokin wajen Rasha Anton Siluanov, ya ce asarar da su ka yi kawo yanzu ta kai dala biliyan dari biyu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu