EU za ta yi taro kan rikicin Ukraine | Labarai | DW | 25.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta yi taro kan rikicin Ukraine

Kungiyar tarayyar Turai ta kira taro na gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen da ke cikin kungiyar don tattaunawa kan sabon rikicin da ya barke a gabashin Ukraine.

Kantomar da ke kula da harkokin kasashen ketare ta kungiyar ta EU Federica Mogherini ta ce a wannan Alhamis din da ke tafe ce za a gudanar da wannan taro da nufin samo hanyoyin warware wannan sabon tashin hankalin.

A 'yan kwanakin da suka gabata gabashin Ukraine din ya fuskanci rikici da ya yi sanadin rasuwar mutane da dama musamman ma a Mariupol a ranar Asabar bayan wani hari da aka kai na rokoki.