EU za ta taimaka wa Afirka magance tsaro | Labarai | DW | 27.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta taimaka wa Afirka magance tsaro

Hukumar tarayyar Turai za ta hada hannu da kasashen Afirka don magance rikicin Libya da sauran kasashe a nahiyar

Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula Von der Layen ta yi alkawarin taimakawa kungiyar tarayyar Afirka magance rikice rikice a nahiyar da suka hada da rikicin kasar Libya.

Von der Layen ta baiyana ta baiyana hakan ne a yau Alhamis yayin ziyarar da ta kai hedikwatar kungiyar tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Ta ce kasancewar tarayyar Turai na tare da kungiyar hadin kan Afirka abu ne mai muhimmanci wajen wanzar da cigaba a nahiyar.

Kokarin kawo karshen rikicin Libya misali ne na kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kungiyar tarayyar Turai da kungiyar hadin kan Afirka.