EU za ta janye cibiyar kudi daga Landon | Labarai | DW | 13.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta janye cibiyar kudi daga Landon

Kwamitin gudanarwa na Kungiyar EU ya sanar da shirin dauke wasu cibiyoyin hada-hadar kudi daga Landon zuwa cikin kasashen Kungiyar bayan aiwatar da matakin ficewar Birtaniyar daga cikin EU.

Kwamitin gudanarwa na Kungiyar Tarayyar Turai ya sanar da shirin gabatar wa kasar Birtaniya da sabbin matakai da Kungiyar EU ke shirin dauka na maido da wasu ayyukan hada-hadar kudi daga birnin Landon zuwa cikin kasashen Kungiyar bayan aiwatar da matakin ficewar Birtaniyar daga cikin Kungiyar. 

Sabon matakin zai bai wa Kungiyar ta EU damar dauke cibiyar hada hadar kudin daga birnin na Landon zuwa wasu cibiyoyin kasashen na Turai wadanda ke a matsayin kafa mafi girma wajen samar da kudaden shiga da kuma ke taimakawa ga kare tsarin kudaden kasashen na Turai. 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan Birtaniya da Kungiyar EU su bude zaman tattaunawa kan aiwatar da shirin ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar, a kuma daidai loakcin da Firaministar kasar ta Birtaniya Theresa May ke shirin ganawa da shugabar jam'iyyar DUP ta Aylan ta Arewa domin samun hadin kan jam'iyyarta mai kujeru 10 a majalisa a kokarin kafa sabuwar gwamnati bayan komabayan da ta samu a zaben 'yan majalisar dokoki.