EU za ta hukunta wasu kasashen Turai | Labarai | DW | 13.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta hukunta wasu kasashen Turai

Kungiyar EU na shirin daukar matakin ladabtarwa kan kasashen Hangari da Poland da Jamhuriyar Chek dangane da kin mutunta yarjejeniyar raba 'yan gudun hijira tsakanin kasashe mambobinta

Kungiyar tarayyar Turai na shirin daukar matakin ladabtarwa kan kasashen Hangari da Poland da jamhuriyar Chek dangane da kin mutunta yarjejeniyar da kasashen Turan suka cimma a watan Disambar shekara ta 2015 wacce ta tanadi cewa wadannan kasashe uku su karbi bakunci wani kaso na yan gudun hijira da a yanzu haka ke a kasashen  Italiya da Girka. 

Kwamishinan kula da harakokin 'yan gudun hijira na Tarayyar Turai Dimitris Avramopoulos ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da ya kira a majalisar dokokin Turai da ke a birnin Strasbourg

Ya ce mun fito fili karara, mun kaddamar da matakin shirin ladabtar da kasashen da ba su dauki alkawari na karbar bakin ba shekara guda bayan cimma yarjejeniyar rarraba 'yan gudun hijirar a tsakanin kasashenmu

A watan Disembar shekara ta 2015 ne dai a wani mataki na rage wa kasashen Girka da Italiya nauyin 'yan gudun hijirar sama da miliyan daya da suka shigo cikinsu, Kungiyar ta EU ta dauki matakin rarraba 'yan gudun hijirar dubu 160 da ke girke a kasashen Italiya da Girka a tsakanin kasashe mambobinta a cikin shekaru biyu. Sai dai har ya zuwa yanzu kasa da dubu 21 ne kawai sauran kasashen Turan suka karba.