1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta hana shigar da makamai Libiya

Ahmed Salisu
January 20, 2020

Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ta EU sun amince da su mayar da hankali kan sintiri da suke yi a Tekun Bahar Rum don ganin sun toshe dukannin wasu kafofi da amfani da su wajen fasakaurin makamai zuwa kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/3WVxz
Libyen Symbolbild Regierungssoldat
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Kantoman da ke kula manofofin kasashen ketare na EU din Josep Borrell ne ya ambata hakan bayan kamamla zama da ya yi da ministocin kasashen ketare na kasashen da ke kungiyar kan rikicin na kasar ta Libiya.

Baya ga batun dakile shigar da makamai kasar ta Libiya, Borrell ya ce EU za ta yi bakin kokarinta wajen ganin an tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin bangarorin da ke kai ruwa rana a kasar.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan wani zama na musamman da aka yi a birnin Berlin na tarayyar Jamus kan rikicin Libiya din, wanda ya samu halartar shugabanin wasu kasashen duniya da kuma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya gami da shugaban kungiyar kasahen Afirka ta AU.