1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta hada kai da gabashin Afirka kan bakin haure

Mohammad Nasiru AwalApril 14, 2016

Kungiyar tarayyar Turai za ta tattauna da wasu shugabannin kasashen gabashin Afirka kan batun mayar da bakin haure.

https://p.dw.com/p/1IW7J
EU-Staaten Streit um Flüchtlingsfrage
Hoto: picture-alliance/dpa/MOAS.EU/ Darrin Zammit Lupi

Duk da shakkun da take nunawa da kanta, kungiyar Tarayyar Turai EU za ta shiga tattaunawa da shugabannin kasashen gabashin Afirka game da mayar da 'yan gudun hijira da bakin haure daga wadannan kasashe. Wata kafar yada labarun Jamus ta tsegunta labarin da ta ce sahiha ne. Karkashin shirin mayar da 'yan gudun hijirar hukumar zartaswar Tarayyar Turai da hukumar kula harkokin ketare ta EU sun ba da shawarar neman hadin kai da shugabannin kasashen Eritriya da Sudan da Habasha da kuma Somaliya. Karkashin shirin hadin kan dangane da manufofin 'yan gudun hijirar, Tarayyar Turan za ta saka wa wadannan kasashen da jerin taimakon tattalin arziki da rage musu wahalhalun neman bisa musamman ga jami'an diplomasiyyarsu. A wani taron jakadun kasashen EU da ya gudana a ranar 23 ga watan Maris aka gabatar da shawarwarin da ba so su bayyana ga jama'a ba.