EU za ta bayyana tsarinta na yaƙi da baƙin haure | Labarai | DW | 13.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta bayyana tsarinta na yaƙi da baƙin haure

Akwai dai saɓannin ra'ayoyi tsakanin ƙasashen a kan tsarin wanda ya ƙunshi dokoki da dama.

Wakilai na kwamitin Ƙungiyar Tarrayar Turai za su bayyana tsarin da suka yi a yau a birnin Brussel na Beljium,na aikin yaƙi da baƙin hauren da ke tsalakawa daga nahiyar Afirka ta tekun Baharum zuwa Turai.

Ana dai samun saɓanin ra'ayi tsakanin ƙasashen a kan batun addadin da aka ƙaide wanda ya zama dole ga ƙasashen kungiyar ta EU,na ɗaukar nauyin wasu daga cikin baƙin hauran da suka canacanci samun matsayi na yan gudun hijira.Italiya wacce ta gabatar da wannan buƙata na samun goyon bayan jamus da Faransa.Amma Birtaniya tare da wasu sauran ƙasashe na arewacin Turai na yin adawa da tsarin