EU: Yarjejniyar karbar bakin haure | Labarai | DW | 31.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Yarjejniyar karbar bakin haure a Turai

EU: Yarjejniyar karbar bakin haure

Kungiyar Tarayyar Turai ta cimma wata matsaya kan batun karbar bakin haure 131 da aka ceto daga teku, wadanda suka jima makale a jirgin ruwan Italiyan da ya cecesu Gregoretti sakamakon kin karbarsu daga kasashen Turai.

Kasashen Faransa Jamus Portigal Luxemburg da Irland, tare da tallafin Cocin Italiya ne suka cimma wannan yarjejeniya a yau Laraba, a wani yunkuri na kawo dauki ga bakin hauren 131, da suka jima suna gararamba a cikin jirgin a gabar tekun Sicile na Italiya ba tare da wata kasa ta karbesu ba.  

Duk da yake ya zuwa yanzu kungiyar bata fayyace yadda za a rarraba adadin bakin hauren ba, rahotanni sun ce galibin bakin hauren da aka ceton za su kasance ne a kasar Italiya inda babbar Cocin kasar za ta dauki nauyinsu.