EU ta yi watsi da buƙatar taimakawa ′yan tawayen Siriya da makamai | Labarai | DW | 18.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta yi watsi da buƙatar taimakawa 'yan tawayen Siriya da makamai

Kasashen Tarayya Turai sun tsawaita takunkumin haramta shigar da makamai a Siriya.

Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service Syria's President Bashar al-Assad (R) meets International peace envoy for Syria Lakhdar Brahimi in Damascus December 24, 2012 in this handout photograph released by Syria's national news agency SANA. Brahimi met with Assad in Damascus on Monday to discuss a solution to the country's 21-month-old conflict. Brahimi told journalists after the meeting that he discussed the situation in Syria overall and gave his views on how to solve the crisis. He said conditions in the country were still poor. REUTERS/Sana (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS

Assad da Lakkdar Brahimi

Mafi yawan ƙasashen ƙungiyar Tarayya Turai, sun yi watsi da bukatar ɗage takunkumi shigar da makamai a Siriya, domin taimakawa 'yan tawaye.

A taron da suka shirya yau a birnin Brussels, ƙasashen EU sun ce ɗaukar matakin ɗage takunkumin zai ƙara dagula al'amura a wannan ƙasa da ke fama da yaƙe-yaƙe shekaru biyu kenan da su ka gabata.Ranar ɗaya ga wata mai kamawa, wa'adin takunkumin haramtawa Siriya makamai ke kai ƙarshe saidai EU ta baiyana mahimmancin tsawaita wannan wa'adi.

A wani labarin kuma da ya shafi Siriya,yau ne Komitin da Malisar Dinkin Duniya ta girka domin binciken rikicin Siriya, ya gabatar da rahotonsa a birjin Jeneva na ƙasar Switzerland.

Karla del Ponte, tsohuwar mai shigar da ƙara a kotin ƙasa da ƙasa mai hukunta mayan lefika bugu da ƙari memba a cikin wannan komiti ,ta ce ƙarara sun gano kisan kiyasun da aka aikata a Siriya, kuma lokaci ya yi na gurfanar da masu hannu a cikin wannan ɗanyan aiki gaban kotun ƙasa da ƙasa mai hukunta manyan lefika dake birnin Hague ko kuma La Haye na ƙasar Holland.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal