EU ta tsawaita takunkumi wa Rasha | Labarai | DW | 01.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta tsawaita takunkumi wa Rasha

Kungiyar Tarrayar Turai ta kara tsawaita wa'adin takunkumin karya tattalin arziki da ta kakaba wa Rasha tun a shekara ta 2014 saboda zarginta da hannu a yakin Ukraine

Ilahiran manbobi na Kungiyar ta EU sun amince da kara wa'adin har ya zuwa ranan 31 ga watanan Janairu na shekara ta 2017. Wa'adin na farko wanda ke kammala a karshe wannan wata ya shafi hada-hadar bankuna na Rashar da kamfanonin samar da man fetir da kuma harkokin tsaro.

Kasashen sun ce har yanzu Rasha ta yi fatali da yarjejeniyar da aka cimma a birnin Minsk na ganin ta bayar da gundunmowarta wajen samar da zaman lafiya a gabashin Ukraine.