EU ta tsara matakin hana shiga daga Libiya | Labarai | DW | 17.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta tsara matakin hana shiga daga Libiya

Kungiyar tarayyar Turai, ta amince da takaita samar da kwale-kwale da wasu injunan ruwa zuwa kasar Libiya a kokarinta na dakile kwararar baki zuwa wasu kasashen yankin.

Ministocin harkokin waje na kasashen da ke kungiyar Turai, sun amince da matakin takaita shigar da kwale-kwale da ake hura wa iska da ma wasu masu inji, zuwa kasar Libiya. Wannan dai mataki ne na dakile shigar bakin haure daga kananan kasashe zuwa nahiyar Turan.

Sama da mutane dubu 100 ne dai hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya ta ce suka ketara kogin Baharrum zuwa kasashen. Kungiyar ta EU ta kuma ce matakin zai maganta fasa-kaurin jama'a da wasu bata-gari ke yi. Matakin dai zai hana amfani da kwale-kwale ga mutane musamman masunta da masu sarafar kayayyaki.

Sai dai fa wasu bayanan na cewa, wannan matsala ta shigar irin wadannan kwale-kwalen, na faruwa a wasu kasashe makwabtan kasar ta Libiya.