EU ta tallafa wa Nijar a yaki da ta′addanci | Siyasa | DW | 05.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EU ta tallafa wa Nijar a yaki da ta'addanci

Tarayyar Turai ta tallafa wa Nijar da kudi har miliyan 36 na Euro domin yaki da ta'addanci dama safarar bakin haure zuwa Turai.

Toter Soldat in Mangaizé

Harin 'yan ta'adda a Nijar

A jamhuriyra Nijar gwamnatin kasar ta kulla wata yarjejeniya da Tarayyar Turai domin tallafa wa kasar kan fannoni daban daban da suka shafi tsaro, matsalar bakin haure da farfado da wasu fannnoni irin su kiwon lafiya da kyautata rayuwar al’umma.

Tallafin da Tarayyar ta Turai ta ware wa Nijar na kimanin Euro miliyan 36 na daya daga cikin tallafi mafi karfi da hukumar ke bai wa wasu kasashen Afirka da suka rattaba hannu da ita a yarjejeniyar ACP wannan kuwa da niyar kama wa Nijar din yin fito na fito da wasu mahimman matsaloli ire-iren su yaki da ta’addanci da matsalar kwararar bakin haure da kyautata wasu fannonin rayuwar al’umma kamar matsalar kiwon lafiya da ilimi da kare muhalli.

Dama kasar na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba gaba a tsarin tallafawa da Tarayyar Turai ke yi wa wasu kasashen Afirka ko dai dan saboda kasancewa mafi saukin wucewa daga wasu matasan kasashen nahiyar domin tsallakawa Turai ko kuwa dai kasar ta na daga cikin mafi kasancewa cikin hadari a Yammacin Afirka ganin yanda take zagaye da kasashen da tashe- tashen hankula da fitintinu irin na ta’addanci suka fi kamari.

Europäische Entwicklungstage Barroso und Sierleaf 26.11.2013

Taron EU da Nijar kan yaki da ta'addanci

Daga shekarun 2014 zuwa 2020 Nijar za ta ci moriyar Tarayyar Turai da tallafin kudade kimanin Euro miliyan 596 a wasu mahimman ayyukan da suka hada da gyaran hanyoyi da matsalar fari ko karamcin abinci da talafa wa kungiyoyin farar hula da batun wanzar da zaman lafiya inda Tarayyar ta Turai za ta bayar da kudden ta hanyar tallafa wa kasasfin kudin jamhuriyar Nijar.

Karin bayani kan dalillan EU na bada tallafin

A jawabin da ta gabatar a gurin bikin sanya hannu kan wannan yarjejeniya Shugabar sashen kula da harakokin kasashen waje ta Tarayyar Turai Neven Mimica ta yi karin haske kan tallafin nasu tana mai cewa:

"Ta ce mun amince da kara yawaita tallafin kasafin kudin ne na Nijar don kara karfafa wa kasafin kudinta na shekara ta yanda hakan zai bata dammar inganta fannoninta na tsaro da kiyon lafiya da duk wasu fannoni na inganta rayuwar alummar kasa .Ta ce kuma za mu kiyaye domin bin kudaden sau da kafa wajan ganin gwamnatin kasar ta sakasu a inda ya kamata domin inganta rayuwar yan kasarta kamar yanda yarjejeniyar ta tanada".

Martanin gwamnatin Nijar kan tallafin na EU

Tallafin dai tuni ya samu guda da yabo daga bangarorin hukumomin kasar Nijar da suka ce za su amfani da dukiyar a wuraren da suka kamata. Hajiya Aichatou Kane Boulama ita ce ministar harkokin wajen Nijar ta ce faduwa ce ta zo dai dai da zama.


Niger Agadez Sahara Flüchtlinge

Safarar bakin haure ta Saharan Nijar zuwa Turai

"a ce duk wadanga abubuwan da kuka gani wani harkar bakin haure wata harkar tsaro ko ta gurbatar yanayi su na kawo cikas a fannin tattalin arziki kenan wannan abin ya na kawo wa kasarmu cikas a fannin tattalin arzikinta, kenan shawo kan wadannan matsalolin ya na da mahimmanci ka ga kenan a game da kokarin da muke na duk wadannan abubuwan suka ce za su kawo muna goyon baya bisa kan kokarinmu da hanyoyin da mu ka bi suka ce za su kawo muna tallafinsu, domin idan ka ce za ka kula da tsaro to dole ka dauki kudi ka sakasu a cikin harkar tsaro."


Wasu alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nunar da cewa sama mutum dubu 4500 ne 'yan kasashen Afirka ke ratsawa ta hamadar Nijar akalla ko wani mako inda galibinsu ke tsallakawa zuwa Turai, ko ba’idinsu a yanzu an kiyasta wasu sama da dubu 80 da ke neman ketarawa a wannan shekarar. Nijar ta bakin ministar harkokin wajenta ta ce ta na shirye domin kawo nata kokari a yunkurin da tarayyar turai take na dakile matsalar ta bakin haure:

Damuwar gwamnatin Nijar kan batun bakin haure

Niger Agadez Sahara Flüchtlinge

Safarar bakin haure ta Sahara zuwa Turai

"anan matsalar ta bakin haure ta na da dagantaka da wasu mayan kungiyoyin bata gari da ke kawo matsala a cikin harkokin bunkasar kasarmu da saura wasu kasashenmu abin da muka sa a gaba shi ne mine ne ke sa 'yan kasashen ke fita zuwa wasu kasashe daga kasashensu to shi ne muka sa a gaba kuma shi ne ya kamata a kawo wa magani".


Sai dai tallafin na tarayyar turai na zuwa ne a yayin da batun tsaro a kasar musamman a yankin Diffa mai fama da matsalolin Boko Haram ke ci gaba da daukar hankali inda a baya bayannan ma a garin dagaya yan kungiyar suka yi wa askarawan Nijar kwantan bauna wanda har suka hallaka sojan kasar daya. Sai dai rahotanni sun ce sojojin sun mayar da martani ta hanyar ruwan boma bommai ta sama da wasu jiragen yaki biyu a garin na Dagaya inda abin ya faru, labarin da har yanzu hukumomin yankin ba su ce uffan ba dangane wannan batu.

Sauti da bidiyo akan labarin