EU ta tallafa wa Italiya saboda girgizar kasa | Labarai | DW | 30.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta tallafa wa Italiya saboda girgizar kasa

Kwamitin kasafi na majalisar ya amince da bada wannan kudi daga asusun hadaka na Kungiyar EU, wato daga kudaden da ake amfani da su wajen tallafawa mambobi.

Majalisar Kungiyar Tarayyar Turai a wannan rana ta Laraba ta amince da bada kudi tsaba Euro miliyan dubu da dari biyu don tallafa wa al'umma da suka fiskanci bala'in girgizar kasa a Italiya a shekarar bara da wannan shekara.

Kwamitin kasafi na majalisar ya amince da bada wannan kudi daga asusun hadaka na Kungiyar EU, wato daga kudaden da ake amfani da su wajen tallafawa mambobi na kungiyar da suka fiskanci wani bala'i.

Girgizar kasa da aka rika samu daga watan Agusta 2016 zuwa Janairu 2017 ta shafi al'umma da dama a Tsakiyar Italiya. Fiye da mutane 330 suka rasu yayin da sama da 30,000 suka kauracewa muhallansu, baya ga wadanda harkokin kasuwacinsu ya gurgunce.