1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta soki tarzoma a zaben Venezuela

July 31, 2017

Kungiyar tarayyar Turai ta baiyana damuwa game da makomar dimokradiyya a kasar Venezuela bayan zaben wakilan majalisar shawara ta kasa da ya sha suka.

https://p.dw.com/p/2hScS
Venezuela Proteste
Hoto: Imago/ZUMA Press/J. C. Hernandez

Kungiyar tarayyar Turai ta baiyana damuwa game da makomar dimokradiyya a kasar Venezuela bayan zaben wakilan majalisar shawara ta kasa da ya sha suka.

Mai magana da yawun hukumar tarayyar Turai Mina Adreeva ta ce irin wannan majalisa wadda aka zaba a yanayi na shakku da kuma rudani ba za ta kasance masalaha ba.

Andreeva ta ce tarzomar zaben na karshen mako wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum goma zai kara sanya rashin halasci a dimokradiyyar Venezuela da hukumominta.

Shi ma Shugaban majalisar dokokin Turai Antonio Tajani yace kungiyar tarayyar Turai ba za ta amince da sakamakon zaben ba. 

Kungiyar tarayyar Turan ta kuma yi Allah wadai da amfani da karfi fiye da kima da jami'an tsario suka yi akan masu zanga zangar adawa da zaben..