EU: Ta sanar da sunayen kwamishinoninta | Siyasa | DW | 11.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EU: Ta sanar da sunayen kwamishinoninta

Shugabar hukumar zartaswar tarayyar Turai mai jiran gado, Ursula von der Leyen ta gabatar da jerin sunayen kwamishinonin hukumar da za su aiki tare a cikin shekaru biyar masu zuwa.

A ranar Talata shugabar hukumar zartaswar tarayyar Turai mai jiran gado, Ursula von der Leyen ta gabatar da jerin sunayen kwamishinonin hukumar da za su aiki tare a cikin shekaru biyar masu zuwa. Sabuwar shugabar hukumar ta kira tawagar kwamishinoni da cewar an yi raba daidai tsakanin jinsuna, an kuma yi la'akari da yankunan siyasa na Turan.  A ranar daya ga watan Nuwamba mai zuwa sabbin kwamishinonin da sabuwar shugabar hukumar zartaswar ta Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta nada za su fara aiki matukar sun sami amincewar majalisar dokokin Turai. Bisa la'akari da jerin sunayen kwamishinonin da suka hada da mata 13 da maza 14 ana iya cewar von der Leyen da ke zama tsohuwar ministar tsaron tarayyar Jamus, ta cika alkawarin da ta dauka na samun daidaito a cikin hukumar mai wakilai 27, kamar yadda ta nunar a lokacin gabatar da jerin sunayen.

    Ursula von der Leyen ta cika alkawarin da ta dauka na samun daidaito na mukamai tsakanin maza da mata a hukumar EU

Shugabar hukumar zartaswar tarayyar Turai mai jiran gado, Ursula von der Leyen

Shugabar hukumar zartaswar tarayyar Turai mai jiran gado, Ursula von der Leyen

Ta ce: "Ina son wannan hukuma ta zama mai daidaito tsakani jinsuna da kuma ta kunshi dukkan yankunan siyasa na Turai. Kamar yadda kuka ganin mataimakan shugaba sun fito daga gabas da yamma sai kuma kudu da arewa na tarayyar Turai. Ina son hukumar tarayyar Turai ta zama mai kare dukkan muradu na al'umma. Jami'ai a birnin Brussels hedkwatar tarayyar Turai sun ce sabuwar hukumar ta EU za ta karkafa yaki da sauyin yanayi karkashin jagorancin Frans Timmermans mai shekaru 58 dan kasar Holland kuma kwararren jami'i a Brussels.

Sauti da bidiyo akan labarin