EU ta kasa cimma matsaya kan bakin haure | Labarai | DW | 18.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta kasa cimma matsaya kan bakin haure

Taron ministocin cikin gida na kasashe mambobin Kungiyar Tarayyar Turai kan batun 'yan gudun hijira da ya gudana a ranar Laraba a birnin Helsinki na kasar Finland ya kawo karshe ba tare da cimma matsaya ba. 

Kasashen Faransa da Jamus ne dai suka kira wannan taro da nufin daukar matakin dakatar da haramcin da wasu kasashen Turan ke yi wa jiragen ruwa masu aikin ceto bakin haure a kan teku, a game da shiga tashoshin ruwan kasashensu domin sauke mutanen da suka ceto da kuma tattauna batun rarraba 'yan gudun hijirar a tsakanin kasashen na Turai. 

Sai dai ministan cikin gidan kasar Italiya Matteo Salvini ya yi tsayiwar gwamin jaki kan matsayin kasarsa na adawa da shigar jiragen ruwan masu aikin ceton bakin hauren akan teku a tashoshin ruwan kasar.