1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kalubalanci Poland a gaban kotu

Gazali Abdou Tasawa
September 24, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai ta kalubalanci kasar Poland a gaban kotun Turai a game da wani gyaran fuska da gwamnatin kasar ta Poland ta kaddamar kan kotun kolin kasarta.

https://p.dw.com/p/35PDQ
Polen Justizreform - Richterrobe
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS/P. Twardysko

Matakin rage shekarun tafiya ritaya daga shekaru 70 zuwa 60 da gwamnatin Poland ta yi ga dokar tsarin aikin kotun kolin kasar na daga cikin muhimman matakan da kungiyar ta EU ke adawa da su a kwaskwarimar da gwamnatin ta Poland ta yi wa dokar, wanda kuma kungiyar ta EU ta ce ya saba wa dokokinta. 

Kungiyar ta EU ta bukaci kotun Turan da ta dauki matakin wucen gadi na maido da kotun kolin kasar ta Poland kan tsohon tsarinta na kafin gyaran huskar da aka yi mata a ranar uku ga watan Afrilun 2013. Kana ta bukaci kotun ta Turai da ta gaggauta daukar matakin dindindin kan wannan batu. 

Sabon gyaran fuskar da mahukuntan kasar ta Poland suka yi wa kotun kolin kasar za su tilasta wa alkalai 27 daga cikin 72 da kotun ta kunsa tafiya ritaya matakin da Kungiyar ta EU ta ce katsalandan ne a harakokin shari'a wanda kuma ya saba wa tsarin tafirta.