EU ta kakaba wa Belarus takunkumi
May 25, 2021Talla
Matakin na EU na zuwa ne a wannan Talatar sakamakon abin da mahukuntan birnin Minsk suka yi ranar Lahadin da ta gabata na tursasawa wani jirgin fasinjoji yin saukar gaggawa a kasar tare da kame wani dan adawa da ke kan hanyarsa ta yin bulaguro.
Shuwagabannin kasashen kungiyar sun yi tir da wannan matakin na mahukuntan Belarus din duk kuwa da uzurin da suka bayar na cewa sun tilasta wa jirgin saukar gaggawar ne sanadiyar rahotannin da suka samu na cewa akwai wani abu mai fashewa a cikin jirgin.