EU ta kafa kwamitin tattauna ficewar Birtaniya | Labarai | DW | 14.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta kafa kwamitin tattauna ficewar Birtaniya

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Junker ya kaddamar a wannan Laraba da wani kwamiti na musamman da zai tattauna batun ficewar Birtaniya daga Kungiyar EU.

A cikin wata sanarwa da ya fitar Shugaban kungiyar tarayyar Turan ya ce kwamitin wanda zai kasance a karkashin jagorancin Michel Barnier dan kasar Faransa da kuma Sabine Weyand 'yan kasar Jamus na da nauyin tsara tattaunawa da Kungiyar EU za ta yi da Birtaniya da kuma jagorantar zaman tattaunawar tare da fitar da shawarwari kan yadda dangantaka za ta kasance tsakanin Kungiyar ta EU da Birtaniyar bayan aiwatar da matakin ficewar tata daga kungiyar.

Sai dai kafin soma zaman tattaunawar kan sabuwar dangantakar bangarorin biyu, sai Birtaniya ta kaddamar da shirin soma raba garin da kungiyar ta EU a hakumance , wanda shi kuma ba zai tabbata ba sai a farkon shekara ta 2017.