EU ta jinginar da batun sanya wa Rasha sabbin takunkumai | Labarai | DW | 09.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta jinginar da batun sanya wa Rasha sabbin takunkumai

A taron da suka gudanar a birnin Brussels ministocin kudi na kungiyar EU sun ce za a jira sakamakon taron birnin Minsk kafin a san matakan da za a dauka gaba.

Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar tarayyar Turai sun ce ba za a kakaba wa Rasha sabbin takunkumai yanzu ba. A wani taron da suka yi a birnin Brussels ministocin sun ce ya kamata a jira sakamakon taron kolin da zai gudana wannan Larabar a birnin Minsk na kasar Belarus, inda shugabannin kasashen Rasha da Ukraine da Jamus da kuma Faransa za su duba batun tsagaita bude wuta a rikicin gabashin Ukraine. Frank-Walter Steinemeier shi ne ministan harkokin wajen Jamus cewa yayi.

"Ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron birnin Minsk. Muna fata taron zai gano bakin zaren warware batutuwan da ke hana ruwa gudu."

Sai dai da farko ministocin sun amince a kara sunayen wasu mutane 19 a jerin wadanda EU ta sanya wa takunkumi. Ana zarginsu da tallafa wa 'yan aware magoya bayan Rasha a gabashin Ukraine.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo