EU ta gabatar da ƙudurin hukunta Iran | Labarai | DW | 25.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta gabatar da ƙudurin hukunta Iran

Ƙasashen turai sun gabatar da wani saban ƙuduri ga komitin sulhu na MDD, wanda ya tanadi sabin matakan hukunta Iran, a game da taurin kan da ta nuna, na ƙin watsi da aniyar malakar makaman nuklea.

Ƙasashen turai sun samu saɓanin ra´yoyi da Amurika, a game da wannan batu.

Amurika na buƙatar Russie, ta dakatar da ayyukan da ta ke, a wasu tashoshin samar da makamashin nukleya a ƙasar Iran, matakin da bai samu tabaraki ba, daga EU.

Ƙudurin da rukunin ƙasashen turai su ka gabatar, ya tanadi saka takunkumi ga ƙasasr Iran, da kuma hana wa shugabanin ta, visan shiga turai.

A ɗaya hanun kuma EU, ta ƙudurci katse duk wasu hulɗoɗi da su ka shafi tallafin kuɗaɗe ga Iran, muddun ta ci gaba da yin kunen uwar shegu, a game da batun mallakar makaman nuklea.