EU ta fara taimaka wa shirin zaman lafiya a Filato | Siyasa | DW | 13.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EU ta fara taimaka wa shirin zaman lafiya a Filato

Kungiyar ta ce tuni har ta tsara wasu shirye-shirye da za ta aiwatar tare da samun taimakon hukumomin kasashen ketare irin su GIZ ta Jamus don cimma wannan buri.

Kungiyar tarayyar Turai din dai ta ce ya zuwa yanzu ta tsara manufofin da za ta aiwatar domin ganin cewar zaman lafiya mai dorewa ya samu a jihar Filato dake arewacin Najeriya.

Wasu daga irin manufofin, su ne ta fuskar ilimi, tattalin arziki da kuma yankurin sasantawa tsakanin kabilu daban-daban dake jihar.

Rage zaman kashe wando

Ta fannin ilimi dai kungiyar ta EU ta ce za ta himmatu wajen horas da mallamai, bada kayayyakin karatu da kuma kyautata yanayi da dalibai kan nemi ilimi a jihar.

Ko yaya kungiyoyi na jama'a ke kallon wannan yunkuri? Mr. Guard Shamaki, jami'in

Jos, Plateau-State, Christen und Muslime, Nigeria Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 10. August 2010 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Jos, Nigeria

Garin Jos a jihar Filato

wata kungiya ce mai fafutikar zaman lafiya, yayi karin bayani inda ya ce "wannan kudiri na kungiyar ta tarayyar Turai ya kamata ya sami goyon bayan kowa da kowa a jihar".

Batun tattalin arziki na daga cikin kudirin kungiyar ta EU inda ta ce za ta bude cibiyoyin koyar da jama'a sana'o'in hannu a yankin Jos ta arewa, kana za ta bude wasu cibiyoyin a garin Tunkus dake karamar hukumar Mikang a kudancin jihar Filato. Wannan a cewar kungiyar wata manufa ce ta kawar da talaucci da rage zaman banza biye kuma da ganin cewar mabiya addinai na rika chudanya da juna a wadannan cibiyoyi. To sai dai a cewar Malam Sani Mudi, wani mai sharhi kan al'amura matakin ta EU zai sami nassara ne kawai idan shugabannin dake da nauyin aiwatar da manufofin za su yi adalci. Dan adalci ne kadai zai kai samun zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Bata gari daga waje ke haddasa fitina

Kungiyar ta EU ta ce za ta hada hannu da wasu kungiyoyi a Najeriya irin su "Search for Common Ground" domin rika shirya tarurrukan zaman lafiya tsakanin al'ummomin da ke yankunan jiha. To sai dai a cewar Sineta GNS Pwajok, matsalar jihar Filato ba ta cikin gida ba ce, ya ce "wasu ne daga waje kan shigo don tada hankulan jama'a don cimma wani buri nasu".

Kasancewar yanzu an soma samun zaman lafiya da walwala tsakanin jama'ar jihar Filato, da fatan wannan yunkuri na tarayyar Turai tare da hukumar GIZ ta Jamus zai haifar da nasara wajen samun zaman lafiya mai dorewa a jihar ta Filato.

Mawallafi: Abdullahi Maidawa Kurgwi
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin