EU ta cimma matsaya kan makomar Birtaniya | Labarai | DW | 15.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta cimma matsaya kan makomar Birtaniya

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun cimma matsaya a hukumance na bude sabon babin tattaunawa kan makomar dangantaka da huldar kasuwanci da Birtaniya.

Da yake bayani a birnin Brussels na kasar Beljiyam, shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Junker ya jinjinawa firamistar Birtaniya Theresa May a kan yunkuri na cimma burinta. Amma ya yi gargadin cewa tattaunawa da za a shiga nan gaba na iya daukar zafi fiye da ta farko.

A daya bangaren bangaren Theresa May da take martani a shafinta na Twitter bayan cimma matsayar ci gaba da tattaunawar, ta ce "Yau an cimma gagarumar nasarar kama hanyar kammala ficewa daga EU a cikin ruwan sanyi, tare da duba makomar Birtaniya bayan ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai."

A watan Yunin shekara ta 2016 ne Birtaniya ta kada kuri'ar raba gardama na neman balewa daga kungiyar EU, sai dai ana sa ran ballewar za ta kai watan karshen watan Maris na shekarar 2019.