EU ta ce ficewar Birtaniya na nan
May 24, 2019Kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ta ce murabus din Firaministar Birtaniya ba zai sauya matsayinta a kan batun ficewar Birtaniyar daga gamayyar kasashen Turan, kamar yadda kasar ta sanya hannu ba.
Shugaban EUn Jean-Claude Juncker ya ce majalisar Turan ta kammala daukar matsaya dangane da bukatar Birtaniyar, lokaci ne kawai ake jira.
A yau ne dai Firaministar Birtaniya Theresa May, ta bayyana cewa za ta ajiye aiki a ranar bakwai ga watan gobe na Yuni.
"A yau ina sanar da cewa ranar 7 ga watan Yuni zan yi murabus daga shugabancin jam'iyyar Conservative da na yi farin cikin rikewa, hakan zai ba da damar zaben sabon firaiminista. Lallai ina ajiye aiki mai daraja a rayuwata. Ni ice firai Minista mace ta biyu, amma tabbas ba ta karshe ba"
Theresa May ta fuskanci matsi daga 'yan kasar a kan shirin ficewa daga kungiyar da aka sani da Brexit.
Sau uku kudurinta ya gaza nasara a majalisar Birtaniyar dangane da ficewar kasar.