EU ta ƙuduri aniyar bada horo ga sojojin Mali
January 28, 2013Ranar 17 ga watan da mu ke ciki ne ƙungiyar Tarayya Turai, ta yanke hukunci tura dakaru a Mali ,domin bada horo ga sojojin ƙasar ta yadda za su iya fuskantar ƙalubalen 'yan ta'ada da ke baraza ga ƙasar.
Sojoji 400 zuwa 450 ne ƙungiyar tarayya Turai za ta turawa a ƙasar Mali, saidai saɓanin dakarun Faransa da ke fafatawa a fagen yaƙi, sojojin na EU za su zama a birnin Bamako domin bada horo ga takwarorinsu na Mali.Babban burin da ake buƙatar cimma shine: sojojin Mali su laƙanci husa'o'in yaƙi domin zuwa gaba su cece ƙasarsu da kansu, domin a cewar Richard Zink shugabar tawagar ƙungiyar tarayya Turai a ƙasar Mali koyar da mutum kamin kifi ya fi ka ba shi kifi a gashe:
Ya ce:Cemma EU ta saba shirya makammacin wannan horo a Afrika.Irin sa ne sojojin Somaliya su ka samu.Kuma a tsukin shekaru biyu, dakarun Somaliya suka laƙanci dubarun gwagwarmaya tare da 'yan ta'ada.
Sakamakon da aka cimma a Somaliya ya nunar da cewa kwaliya ta biya kuɗin sabulu.
Saidai al'amarin ƙasar Mali ya na da sarƙaƙiyya inji Professa Modibo Goita domin a shekarun baya , kasar Amirka ta hiora da sojojin Mali dubarun yaƙi da aiyukan ta'adanci, amma a ka wayi gari sojojin da suka samu horan su ka cenza sheƙa zuwa rundunonin tawaye da na ƙungiyoyin ta'adanci:
"Sojojin da Amurika ta ba horo sun tsere da motoci kira Toyota masu shiga yashi fiye ta 80.Akasarin wanda suka samu horon sun fito daga yankin arewancin ƙasa.
Gwamnati ta amince da hakan, domin kaucewa zargin nuna bambancin launin fata a cikin rundunar soja, da zumar cimma burin haɗin kan ƙasa."
Sojojin da suka samu horo daga Amirka, sun kasance daga shika-shikan da su ka girka ƙungiyar tawayen MNLA mai fafutakar samun 'yancin kan yankin Azawad.
A yanzu babban ƙalubalen da ke gaban tawagar sojojin EU a ƙasar Mali shine faɗakar da dakarun ƙasar game da da mahimmancin haɗin kan ƙasa, biyyaya da kuma sadaukar da kai, abubuwan da ke samun ƙarancinsa a ƙasar Mali inji Panya Harivongs wani soja na ƙasar Faransa da ya jima ya na aiki a Mali,ya ce:
A ƙasashe da dama na Afirka ana shiga aikin soja ne ba dan wai ana shawar aikin ba, a'a saboda da dai kawai a samu wurin cin abinci.
A ƙasar Mali matsalar ta fi tsanani domin babu biyyaya ga girmamawa tsakanin sojojin.Sannan a mafiya yawan ƙasashen Afirka su kansu shugabanin ƙasashe su na da babban lefi a cikin taɓaɓarewar al'amura a rundunar sojoji, domin sun fi daba fifiko ga sojojin dake tsaron lafiyarsu fiye da sojojin da ke tsaron ƙasa.
Ta la'akari da halin da ƙasar Mali ta shiga a yanzu, ƙila ya zama darasi da shugabanin ƙasar da ma na Afirka game da mahimmancin samar da rundunar soja ƙwaƙƙwara wadda za ta kula da tsaron ƙasa.
Mawallafa: Gänsler Katrin da Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe