1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

EU na neman China ta shiga tsakanin yakin Rasha da Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
May 25, 2023

Kungiyar tarayyar Turai ta bukaci jakadan kasar China a kungiyar da ya sanarwa da mahukuntan Sin bukatar neman su taimaka kawo karshen zubda jini da babbar kawarsu Rasha ke yi a kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4RpRi
Enrique Mora | Hoher Vertreter der Europäischen Union
Hoto: Lisa Leutner/AP Photo/picture alliance

Babban jami'in EU a kan harkokin kasashen ketare Enrique Mora wanda ya gana da takwaransa na China Li Hui a birnin Brussels na kasar Belgium ya bukace shi da isar da sakon kungiyar ga mahukuntan Beijing.

China wacce ke zama babbar kawar Rasha ana ganin tana da rawar takawa wajen kawo karshen rikicin da aka shafe watanni 15 ana yin shi.

Kungiyar tarayyar Turai ta ce kasancewar China mamba a kwamitin sulhu na MDD ya kamata ta bada ta ta gudumawar, duk da a cewar a baya China ta nuna ita yar baruwanmu ce a wannan rikicin.

'Yan siyasar EU na nuna shakku a kan shawarwarin da China ta bayar da ka iya kaiwa ga karshen wannan yaki na Turai.