Ethiopian Airlines zai karbi Arik a Najeriya | Labarai | DW | 30.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ethiopian Airlines zai karbi Arik a Najeriya

Shugaban sashin da ke lura da harkokin kasa da kasa a kamfanin Ethiopian Airlines Esayas Woldemariam shi ya bayyana haka a zantawa da kamfanin dillancin labaran AP.

Kamfanin jirgin sama da ke zama kan gaba wajen samun riba a Afirka ya bayyana cewa zai karbi harkokin gudanarwar kamfanin jiragen sama mafi girma a Afirka ta Yamma da ke da cibiya a Najeriya wato Arik Air. Shugaban sashin da ke lura da harkokin kasa da kasa a kamfanin Ethiopian Airlines Esayas Woldemariam shi ya bayyana haka a zantawa da kamfanin dillancin labaran AP, ya ce hakan na zuwa ne bayan da ma'aikatar harkokin sufurin jirgin sama a Najeriya ta gabatar da wannan bukata.

Gwamnatin Najeriya dai ta karbi harkokin gudanarwar kamfanin na Arik a farkon wannan shekara bayan tafka asarar da kamfanin ya yi, don haka a cewar Esayas a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran na AP a shirye suke wajen samar da sauyi a kamfanin.

Kamfanin na Ethiopian Airlines ya kasance daya cikin manyan jirage a Afirka karbar harkokin kamfanin Arik kuma za ta sanya ya sake zama fitacce a Najeriyar da ke da karfin tattalin arziki.