Esperanto | Zamantakewa | DW | 16.11.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Esperanto

Tun karni na 18 ne aka kirkiro wani harshe, mai dauke da wannan sunan, wanda ke da burin zamowa harshe na kasa da kasa da kowa zai iya yin amfani da shi.

Uban esperanto

Uban esperanto

Shirin na yau zai gabatar muku da wani yunkuri da aka dade ana yi ne na kirkiro wani harshe na bai daya, wanda duk duniya za ta dinga amfani da shi. Ba dai karo na farko ke nan ba, da aka fara wannan gwajin, wato na yada harshen wanda aka yi wa suna Esperanto a duk duniya baki daya. Tun da aka kirkiro shi dai, harshen ya sami yaduwa zuwa fiye da kasashe dari na duniya, inda a halin yanzu ake amfani da shi. Sai dai bai zamo harshen hukuma a ko wace kasa ba. Ba dai abin da masu kokarin yada shi ke nufi ke ba nan. Burinsu ne cim ma wata manufa ta sadaswa, inda ko’ina mutum yake, zai iya amfani da wannan harshen, kuma a fahimce shi ba tare da ya sake koyon harshen yanki ko kasar da yake ba. Wato ke nan, ko kasar Larabawa mutumm yake, ko na Turai ko kuma a kasar Sin ko Japan, kai ko’ina ma zai iya amfani da harshen na Esperanto.

To ko ina wannan harshen ya sami asalinsa ? Kuma wane ne ya fara tunanin kirkiro harshe daya da duk duniya za ta iya yin amfani da shi ?

Harshen na Esperanto dai na da asali ne daga kasar Poland. Amma ba harshen kasar ba ne, ko kuma na wasu kabilu. A’a. Harshe ne dai da aka kikiro musamman, wai don ya maye gurbin duk harsunan da ake amfani da su a duniya, ta yadda kowa, ko mene ne ma harshensa na asali, zai iya amfani da shi. Tun fiye da shekaru 125 ke nan da wani dan makaranta a kasar Poland, mai suna Lazarus Ludwig Zamenhof, ya yi tunanin samad harshen kasa da kasa don kyautata cudanya da zaman lumana tsakanin al’ummomin duniya. Wannan tunanin na Zamenhof dai na da dalilai na tarihi. Saboda a garin da aka haife shi, wato Bialystok, a can kasar Poland din, a shekarar 1859, ya tashi ne a lokacin da Rasha ke yi wa yankin mulkin mallaka. Kuma, ban da `yan kasar, akwai al’ummomi da dama, kamrsu Rashawa, da Yahudawa, da Jamusawa da dai `yan sauran wasu kabilun gabashin Turai na wannan lokacin. To sai kuma, ya kasance zamani ne da ake ta rikice-rikicen kabilanci, inda kabilun da ke zaune a garin suka kebe kansu suka kafa unguwanninsu, suna kuma ta nuna kyama ga juna.

A cikin wannan halin ne dai Lazarus Ludwig Zamenhof ya tashi. A cikin rubuce-rubucen da ya yi, Zamenhof ya bayyana dalilan da suka sanya shi tunanin kirkìro harshen na Esperanto ne kamar haka:-

„Wani dan taliki mai fama da kadaici, yana ji yana gani, yadda a cikin wannan garin, fiye da ko’ina ma bambancin harsuna ke janyo tashin hankali. Ko wane taki ya yi, yana lura da cewa, wannan bambancin harsunan ne musababbin ko kuma daya daga cikin muhimman dalilan da ke janyo baraka tsakanin al’ummomi, yake mai da su masu nuna kyama ga juna.“

Ta hakan ne dai Zamenhof, wanda ya koyi sana’ar likita, ya bayyana halin da ake ciki a garin haihuwarsa, Bialystok. A cikin shekarar 1887 ne ya wallafa farkon littafin harshen da ya kirkiro, wanda daga baya aka yi wa lakabin Esperanto. Wannan ra’ayin na Zamenhof dai ya sami karbuwa sosai a wannan yankin na duniya. A cikin shekara 4 kawai, ya wallafa litattafai 33 kan wannan harshen, wadanda aka fasara su zuwa harsuna 12.

A halin yanzu dai, akwai kungiya ma ta duniya da aka kafa, ta masu amfani da wannan harshen. Fritz Wollenberg, shi ne shugaban reshen wannan kungiyar a birnin Berlin a nan Jamus. Ya bayyana cewa, idan aka bi diddigin tarihi, ba a karni na 18 ne harshen na Esperanto ya sami asalinsa ba. Tun kafin wannan lokacin ma, akwai wadanda suka yi tunanin samar wa duniya harshe na bai daya, da nufin ta hakan, su taimaka wajen kau da rikice-rikce da rashin fahimtar juna da ake ta fama da su. Bisa cewarsa dai:-

„A cikin shekarar 1887 ne aka kirkiro harshen, amma tushensa na can baya da hakan. Saboda ya kunshi al’adu ne na mutunci da fadakad da kan al’ummomi. Wadannan ra’ayoyin kuma, tun da dadewa ne masu hangen nesa kamarsu Komensky, da Leibnitz da dai masu imani da tafarkin tabbatad da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomi suka fara yada su, tun kafin dai a kirkiro harshen na Esperanto.“

Kamar dai yadda duk wani sabon salon da ya bayyana, ke huskantar masu yi masa suka da nuna masa adawa, wannan harshen ma ya huskanci daddagewar wasu bangarori, musamman ma dai na siyasa. A kasar Rasha a lal misali, a lokacin mulkin sarakunan nan masu lakabin Tsar, sai da aka haramta buga litattafan harshen, don kada jam’a da ke ta kara nuna sha’awa a kansa, su yi amfani da su. Amma a wasu wuraren kuma, sai harshen ya sami yaduwa, kamar dai a Faransa, inda kusan duk nau’i na al’ummomin kasar ne suka fara amfani da shi. Tun shekarar 1905 ne ma, aka yi farkon taro na duniya kan harshen Esperanton, a garin Boulogne-sur-Mer, a Faransan. Shekara daya bayan haka ne kuma, aka kafa kungiyar masu amfani da harshen a nan Jamus. Kamar yadda Wollenberg ya bayyanar:-

„A Berlin dai, tun shekarar 1908 ne aka sami zaunannun kungiyoyin ma’aikata masu amfani da harshen. Sun dai kara yaduwa ne a lokacin Jumhuriyar Weimar, wato bayan yakin duniya na farko.“

Amma a lokacin mulkin kama karya na`yan Nazi ne, aka fara fatattakar masu amfani da harshen, inda a shekarar 1933, aka haramta duk wasu kungiyoyin da ke da jibinta da wannan salon. Shekaru 5 bayan haka ne kuma aka rufe gidan tarihin harshen Esperanton a birnin Vienna. Har dai ya zuwa shekarar 1945, lokacin da aka kawo karshen yakin duniya na biyu, harshen Esperanto, bai sami yaduwa ba kuma.

Sai bayan yakin ne jama’a da dama, musamman a kasashen Turai suka fara farfado da harshen, suka tsaya daran dakau wajen ganin cewa ya sake yaduwa zuwa sassa daban-daban na duniya. A halin yanzu dai an kiyasci cewa, kusan mutane daga dubu dari 5 zuwa miliyan 10 ne ke amfani da wannan harshen a duk duniya baki daya. Sai dai tun da kirkiro harshen aka yi, ba shi da wane tushe na asali, turawa ne suka fi gane shi. Kusan kashi 60 cikin dari na kalmominsa dai, daga harsuna kamarsu Faransanci da Spanisanci suke, kashi 30 kuma daga Jamusanci, da Ingilishi, da kuma Danisanci, wato harshen kasar Dennmark. Sauran kalmomin ne ke da asalinsu daga harsunan Asiya.

 • Kwanan wata 16.11.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvUQ
 • Kwanan wata 16.11.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvUQ