Ennahda ta sha kaye a zaben Tunisiya | Siyasa | DW | 27.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ennahda ta sha kaye a zaben Tunisiya

Jam'iyyar nan mai ra'ayin musulunci ta Ennahada, ta amince da shan kaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka yi ranar Lahadi a fadin kasar.

Jamiyyar da ba ruwan ta addini Nidaa Tounes a kasar Tunisiya, ta samu nasarar samun kujeru sama da tamanin cikin zaben majalisar dokokin kasar da ke da kujeru 217, inda jam'iyyar masu ra'ayin Islama ta Ennahda ta samu kashi 67 na kujerun a cewar wasu majiyoyin jam'iyyun. cikin sakamakon da suka fara fitowa.

Ranar Litinin ne dai wani babban jami'in jam'iyya mai ra'ayin Islama ta Ennahdah ya ce sun yadda da shan kayi daga jam'iyyar Nidaa Tounes, a zaben na ranar Lahadi.

Matasa sun taka rawar gani a zaben

Al'ummar kasar ta Tunisiya dai ta zabi sabbin mambobin majalisar dokokin kasar, a zaben da ke kara sanya wannan kasa rungumar tsarin dimokiradiya tun bayan kifar da gwamnatin Ben Ali da ta zama dalilin juyin juya hali da aka samu a tsakanin kasashen larabawa.

Bayanai dai na cewa mutane da dama ne ciki har da matasa sun taka rawar gani wajen juyin juya halin kasar ta Tunisiya. kamar yadda wannan masaniya ta fannin shari'a, Lamiya Zargouni take cewa.

"Gaskiya ne cewa matasa ne kashin bayan juyi-juya halin da aka aiwatar da Tunisiya. Amma kuma daga bisani sun yi korafin cewa an mayar da su saniyar ware. jam'iyyun siyasa ba su dama da su ba a kokarin da suke yi na kakkange harkokin mulki. Saboda haka su matasa, ba su san ma manufofin jam'iyyun ba."

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa sama da mutane miliyan 5 da aka yiwa rajista ne suka kada kuri'a a wannan zabe.

Sauti da bidiyo akan labarin