Shekaru 70 na sarautar Elizabeth ta II
June 2, 2022Ana dai matukar mutunta sarauniyar ta Ingila Elizabeth ta II a kasar da ma wasu kasashe na duniya. A cewar galibin al'ummar Ingila da DW ta tattauna da su, sarauniyar ta kwashe tsawon wadannan shekaru 70 tana kokarin sauyawa mutane rayuwa. Mai shekaru 96 a duniya, Elizabeth ta biyu ta kwashe shekarun da aka ce babu wanda ya yi irinsu a kan karagar sarautar a tarihin Birtaniya. Georgina Wagner na cikin wadanda ke jin kamar su zuba ruwa a kasa su sha, saboda yadda suka shaida shekaru 70 na mulkin Sarauniya Elizabeth din: A cikin wadannan shekaru, ta yi kokarin sada zumunci da 'yan uwantaka a kasashen duniya. Ba na tsammanin akwai wani mutum a duniyar nan da ya yi irin abin da ta yi.''
Albarkacin bikin cikar Sarauniya Elizabeth shekarun 70 a kan gadon sarauta, wata cibiya mai kare hakkokin mata a kudancin London ta tara mata da ke saka 'yar tsana mai siffar karen da Sarauniya Elizabeth ta fi kauna a rayuwarta domin su rarraba a fadin kasar. Sarauniyar ta Ingila dai, za ta yi matukar murna da irin wannan kokari da matan ke yi domin mutunta ta. Tun tana karamar yarinya ne dai, soyayyarta ga karnuka ta fito fili. Ko bayan da aka nada ta sarautar Ingila shekaru 70 din da suka gabata, karnukanta da ake yi wa lakabi da corgies sun kasance cikin 'yan fada. Bayanai sun nuna cewa Sarauniya Elizabeth yanzu haka, ta fi kowane basarake dadewa a kan gadon sarauta a duniya. Mai biye mata a dadewa a sarautar Birtaniya dai, ita ce Sarauniya Victoria wacce ta yi mulki na shekaru 63 da watanni bakwai da kwanaki biyu kafin mutuwarta a shekara ta 1901.