1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Elijah mai kera injin sarrafa kayan noma

Uwais Abubakar Idris GAT
October 31, 2018

A Najeriya wani matashi da Allah ya yi wa baiwar kere-kere ya kafa sana'ar kera injina iri-iri na sarrafa kayan noma dabam-dabam da suka hada da na samar da man kade, da man ja da ma na yin garin rogo.

https://p.dw.com/p/37RJt
Nigeria Maisfeld Bewässerung
Hoto: DW


Matashin mai suna Yunana Elijah ya mallaki ma'aikatar kansa ta kera wadannan injina da ke a yanzu haka a unuguwar Karu a jihar Nasarawa. Matashin ya ce ya dukufa aikin kirkiro injinan ne domin saukaka wa mutanen karkara musamman mata wahalhalun da suke fuskanta wajen sarrafa man ja da wajen aikata rogo dan samar da garin rogo ko kuma sarrafa gyada don samar da man girki na gyadar.

Yunana Elijah ya ce ya rungumi wannan sana'a ce a wani mataki na magance zaman kashe wando da ya yadu a tsakanin matasa a Najeriya inda mafi yawancinsu musamman wadanda suka kammala karatu ke zaman jiran samun aiki daga gwamnati, aikin da kuma ba kasafai yake samuwa ba. Wannan sana'a ta kasance wata hanyar da yanzu haka matashin ke dogaro da ita domin daukar nauyin dawainiyar rayuwarsa da ta danginsa.

Ya zuwa yanzu matasa sama da 25 ne ke aiki a karkashin Yununa Elijah inda suke samun 'yan kudaden daukar dawainiyarsu ta yau da kullum, hasalima ya kai ga yae wasu matasan da yanzu haka suka bude nasu ma'aikatun kere-kern suna dogaro da kansu. 

Sai dai matashin ya ce duk da irin ci-gaban da ya samu a cikin wannan sana'a tasa matsalar rashin wadatar lantarki na zama babban kalubale ga sana'ar inda ta kai shi yin amfani a lokutta da dama da injin wuta na janareto.