Egeland ya yi kira da a dakatar da yaki a Libanon na tsawon kwanaki 3 | Labarai | DW | 29.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Egeland ya yi kira da a dakatar da yaki a Libanon na tsawon kwanaki 3

Jami´in dake kula da ayyukan jin kai na MDD Jan Egeland yayi kira ga Isra´ila da Hisbollah da su tsagaita wuta na tsawon sa´o´i 72. Jami´in ya ce hakan zai ba da damar kwashe wadanda suka jikata da yara da tsofaffi daga yankunan da ake batakashi. Bugu da kari za´a kuma samu sukunin kai abinci da magunguna zuwa yankin. Egeland ya ce zai roki Isra´ila da kuma Hisbollah da su dakatar da yakin na wani gajeren lokaci. Jami´in na MDD ya ce fiye da mutane 600, aka kashe a Libanon tun bayan da Isra´ila ta kaddamar da hare hare akan Hisbollah a ranar 12 ga watan na yuli. Egeland ya ce kimanin kashi daya cikin daga cikin wadanda aka kashen yara ne kanana.