1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon gwamnan Adamawa ya gurafana kotu

Zainab Mohammed AbubakarJuly 8, 2015

Murtala Nyako ya kasance tsohon gwamnan Najeriya na biyu da hukumar EFCC ta cafke, bayan takwaransa na jihar JigawaSulei Lamido da kuma 'ya'yansu.

https://p.dw.com/p/1FvKa
Murtala Nyako
Hoto: DW/U. Shehu

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako da dansa Abdu'Azeez da wasu mukarrabansu, a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.

Ana tuhumarsu da laifuffuka 37 na cin hanci da rashawa da fita
da kudadden haramun har naira bilyan 40 mallakar gwamnatin jihar
Adamawa. Murtala Nyako da ya dawo Najeriya bayan gudun hijira tun bayan da aka tsige shi daga kujerar gwamna, ya musanta cewa ya aikata laifin da ake tuhumarsa.

Alkalin kotun mai sharia Ademola Adeniyi ya umurci hukumar EFCC ta ci gaba da tsare Murtala Nyako har zuwa ranar Juma'a 10 ga watan nan don ci gaba da shari'ar.