ECOWAS za ta tura runduna zuwa Mali | Labarai | DW | 12.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ECOWAS za ta tura runduna zuwa Mali

Kungiyar cigaban tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS ta tsai da shawarar tura sojoji 3300 domin ƙwato yankin arewacin Mali.

Bayan wani taro da kungiyar ta yi a Abuja, babban birnin Najeriya jagorarta shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya ce sojojin za su shafe wa'adin shekaru biyar suna aiki a ƙasar. Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Maris ne dai 'yan kishin islama suka ƙwace iko a bakin ɗayan arewacin ƙasar, inda suke neman kafa shari'ar musulunci. Kasashe maƙwabta da kuma ƙasashen yamma na bayyanar da tsoron cewa arewacin Mali ka iya zamewa matattara ga 'yan ta'adda masu kaifin kishin Islama.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi