1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen yankin yammacin Afirka za su fito a kudin bai daya

Abdourahamane Hassane
June 18, 2019

Ministocin kudi na kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ECOWAS su 15 da suka kammaka taro a birnin Abidjan sun tabbatar da cewar a shekara mai zuwa ta 2020 kasashen za su kaddamar da takadar kudin bai daya .

https://p.dw.com/p/3Kerj
Westafrikas Staatschefs bei ECOWAS Summit
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

An dai kwashe sama da shekaru 30 ana jiran ganin an samu kudin na bai daya a tsakanin kasashen. Shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar ta ECOWAS Jean Claude Brou ya ce a wannan jikon ba wani shamaki sai an yi kudin na bai daya na  kasashen yankin yammacin Afirka duk da kalubalen da ya ce ke a gabansu.