1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kan kasashen da sojoji ke mulki

Binta Aliyu Zurmi
July 3, 2022

Shugabannin kungiyar habaka tattalin arzikin Afirka ta Yamma ECOWAS, sun gudanar da taro a kasar Ghana don yin waiwaye kan takunkuman karya tattalin arziki da suka kakabawa kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

https://p.dw.com/p/4Dahl
Afrika ECOWAS Gipfel
Hoto: FRANCIS KOKOROKO/REUTERS

Kasashen na Mali da Guinea da Burkina Faso da yanzu haka ke hannun gwamnatocin rikon kwarya na soja, na fuskantar matsaloli na karayar tattalin arziki.

Babban batun da ya mamaye wannan zauren taron shi ne matsin lamba ga kasashen na Mali da Guinea da Burkina Faso kan komawa  tsarin mulki na dimukuradiyya, kazalika sun tattauna batun sakin hambararren shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore.


Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo da ya karbi bakuncin taron kungiyar mai mambobi 15, ya ce ECOWAS a shirye ta ke ta taimakawa wadannan kasashen don ganin sun zabi halastaciyar gwamnati ta al'umma. 

Daga bisani shugabannin kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO, sun sanar da janye wa gwamnatin sojan kasar Mali takunkuman karya tattalin arzikin da suka kakaba mata bayan da gwamnatin rikon kwarya ta sanar da jadawalin gudanar da zabe da ma komawa kan turbar dimukuradiyya a watan Maris na 2024.