1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An dakatar da Mali daga ECOWAS

Ramatu Garba Baba AMA
May 31, 2021

Shugabanin kasashen yammacin Afirka sun dakatar da Mali daga cikin kungiyar ECOWAS biyo bayan taron kolin da kungiyarsu ta yi birnin Accra na kasar Ghana.

https://p.dw.com/p/3uDta
Ghana Accra| ECOWAS zur Lage in Mali | Nana Akufo-Addo
Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar GhanaHoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images

Matakin da shugabanin kasashen yammancin Afrikan da suka dauka na dakatar da kasar Mali daga cikin Kungiyar ECOWAS na zuwa ne a daidai lokacin da manyan kasashen duniya suka soma gargadin sojojin da suka yi juyin mulki a game da mutunta tsarin dimukuradiyya, bisa fargabar yaduwar rikicin siyasan zuwa sauran kasashe da ke yankin na Sahel masu fama da aiyukan 'yan ta'adda.

Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya nemi shugabanin yankin da su hada karfi da karfe yana mai cewa "Ina kira gareku da kada ku yi kasa a gwiwa har sai an sami mafita daga rikicin Mali, tare da ganin an dora kasar kan turbar dimukuradiyya, kada mu kau da kai daga hadarin da ke tattare da rikicin, saboda haka, ina amfani da wannan dama a madadin kungiyar ECOWAS don jadadda goyon baya ga batun zaman lafiya."

Karin Bayani: Mali: Jerin takunkumi bayan juyin mulki

 Taron ECOWAS  ya kara yin kira ga shugabanin na mulkin soja da su mutunta yarjejeniyar da aka cimma na shirya zabe a watan Febnrairu shekarar 2022 bayan jagorancin mulki na watanni goma sha takwas kamar yadda aka amince tun bayan kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita, wanda ake ganin shi kadai zai fitar da kasar daga cikin wannan rudani, saboda haka masu shiga tsakanin za su ci gaba da aikin tattaunawa da bangarori da dama na kasar ta Mali.

Mali Oberst Assimi Goita, neuer Übergangspräsident
Shugaban juyin mulkin Mali Assimi GoitaHoto: Xinhua/imago images

Kanar Assimi Goita da ya jagoranci juyin mulkin farko a kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita, ya kuma dare madafun iko bayan da ya aiyana kan shi a matsayin shugaban rikon kwarya a ranar Jumma'ar da ta gabata, bai dai yi jawabi ba a yayin taron shugabannin kasashen na yammacin Afirka, sai dai Shugaban Akuffo Addo na Ghana ne ya yi karin bayani yana mai cewa "Wakilai na tawagar kungiyar ECOWAS sun gana da Kanar Assimi Goita, kuma duk kan batun halin da ake ciki ne, da kuma tsara dabaru na shawo kan rikicin.'' 

Karin bayani: Ina aka dosa a rikicin kasar Mali?

Duk da cewa ECOWAS ba ta dauki mataki na kara sanyawa kasar takunkumi kamar yadda ta yi bayan juyin mulkin na farko ba, ta dakatar da kasar daga cikin kungiyar tare da harmatawa duk sojoji da shuganin gwamnatin rikon kwarya shiga takara a zaben da aka tsara gudanarwa a watan Febrairun 2022.

ECOWAS da kasashe kamar su Faransa da ke nazarin barin Mali da Amirka, sun ci gaba da baiyana fargabar yaduwar rikicin siyasar kasar Mali da suka ce ka iya zama babbar barazana ga tsaro, ganin kungiyoyi masu da'awar jihadi irinsu al Qaeda da IS za su iya amfani da halin rashin tabbas a Mali don fadada aiyukansu a yankin.