1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta amince da Ellen Johnson-Sirleaf a matsayin sabuwar shugabar Liberia

November 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvKS

Shugabannin kasashen Afirka ta Yamma sun amince da Ellen Johnson Sirleaf a matsayin zababbiyar shugabar Liberia duk da cewa har yanzu jami´an zaben kasar na duba zargin da tsohon dan wasan kwallon kafa George Weah yayi na tabka magudin zabe. A cikin wani jawabi da yayi ta gidan radiyon Janhuriyar Nijer shugaba Tandja Mamadou wanda kuma shine jagoran kungiyar tattalin arzikin Afrika Ta Yamma wato ECOWAS ya ce a shirye kungiyar ta ke ta yi aiki da Ellen Johnson-Sirleaf ´yar shekaru 67 a matsayin shugabar Liberia. A cikin wani sako da ya aike mata, shugaba Tandja ya ce a madadin sauran shugabanni da gwamnatocin kungiyar ECOWAS ina tabbatar miki da goyon bayan mu wajen sake gina Liberia. Bayan an kidayar dukkan kuri´un da aka kada a zagaye na biyu na zaben da yagudana a ranar 8 ga watannan na nuwamba Johnson-Sirleaf wadda ta yi karatun jami´a a Amirka ta samu kashi 59.4 cikin 100 yayin da abokin takararta George Weah ya samu kashi 40.6 cikin 100. To amma hukumar zaben kasar ta ce ba zata ba da cikakken sakamakon zaben ba sai ta kammala bincike akan zargin da tsohon dan wasan kwallon kafar yayi na aringizo kuri´u.