1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS na tattaunawa kan Ebola da rikicin Burkina

Mariam SissyNovember 6, 2014

Shugabannin ƙasashen Ƙungiyar tattalin arziki na Afirka ta yamma, ECOWAS da ke yin taron yini ɗaya a birnin Accra na Ghana na ƙoƙarin ƙara samar da hanyoyin magance cutar Ebola da kuma rikicin siyasa na Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/1DiSj
Ecowas Afrika Ökonomie Treffen Gipfel Abidjan Elfenbeinküste
'Hoto: Reuters

Shugabanin ƙasashen na tattauna muhimman batutuwan da suka haɗa da gaggauta shawo kan annobar cutar Ebola wacce kawo yanzu ta kashe sama da mutane dubu biyar a cikin wasu ƙasashen Afirka ta yamma. Waɗanda suka haɗa da Laberiya da Gini da Saliyio,da Senegal, da kuma Najeriya.Ko da shi ke ya zuwa yanzu an shawo kan cutar a cikin wasu ƙasashen na Afirka irinsu Senegal da Najeriya, amma dai har yanzu shugabannin na ganin akwai buƙatar a ci gaba da ɗaukar mtakan riga kafi.

Rikicin siyasa na Burkina faso na daga cikin abin da taron zai mayar da hankali

Wakilai na Ƙungiyar za su kuma duba hanyoyin samun bakin zaran rikicin siyasar Burkina Faso, inda sojoji suka kifar da gwamnatin Blaise Compaore a ƙarshen makon da ya gabata.Taron na zuwa kwana ɗaya bayan ziyarar da shugaban ƙasar Ghana kana shugaban Ƙungiyar ECOWAS John Mahama Dramani,ya kai a birnin Ouagadougou na Burkina Faso tare da rakiyar shugabannin ƙasashen Najeriya da Senegal wato Goodluck Jonathan da Macky Sall inda suka gana da Lt. Col. Isaac Yacouba. Mutumin da sojojin Burkina Faso suka wakilta domin jagorancin gwamnatin bayan faɗuwar gamnatin Blaise Compaore wanda suka tattauna batun girka gwamnatin riƙon ƙwarya.

Gipfeltreffen der Westafrikanischen Wirtschaftsgemeinschaft (Ecowas)
Hoto: AFP/Getty Images