1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebrahim Raisi ya samu tikitin takara a Iran

May 25, 2021

Hukumar zabe a Iran ta tabbatar da Ebrahim Raisi da ke zama na hannun damar Ayatollah Khamenei a matsayin dan takarar shugaban kasa, bayan da ta yi watsi da na tsohon shugaban kasa Mahmoud Ahmadinejad.

https://p.dw.com/p/3twih
Iran - Ebrahim Raisi wurde offiziell zum neuen Justizchef Irans ernannt
Hoto: Mizan

Hukumar zaben Iran ta yi watsi da takarar kaso 98 cikin dari na 'yan takarar kujerun shugabacin kasar da na 'yan majalisu cikinsu har da tsohon shugaban kasar Mahmoud Ahmadinejad da mataimakin shugaban kasar mai ci Eshaq Jahangiri da kuma tsohon kakakin majalisar dokokin kasar Ali Larijani.

Cikin wadanda aka yi watsi da takarar tasu sun hada da Mostafa Tajzadeh wani da ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin gwmanatin Shugaba Hassan Rohani da kuma dukkanin mata 40 da suka tsaya takara a zaben.

Sai dai hukumar ta amince da takarar Ebrahim Raisi babban jojin kasar kuma na hannun damar shugaban addinin kasar ta Iran  Ayatollah Ali Khamenei a matsayi dan takarar shugabancin kasar kuma daya daga cikin 'yan takarar da za su tsaya a zabukan kasar masu zuwa. A ranar 18 ga watan Juni mai zuwa ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Iran.