Ebola ta sake bulla a Saliyo | Labarai | DW | 05.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola ta sake bulla a Saliyo

A Saliyo murna na neman komawa ciki bayan da aka samu sabon rahoton bullar cutar Ebola mai saurin kisa a kasar.

Wata mata mai kimanin shekaru 67 a duniya ce ta rasa ranta a sakamakon cutar ta Ebola a kauyen Kambia. Wannan dai ya sanya tuni aka kebe baki dayan al'ummar kauyen domin dakile sake yaduwarta tamkar wutar daji, yayin da ake sanya idanu sosai a kan akalla mutane 1,000. Rahotanni sun nunar da cewa matar wadda ke sana'ar sayar da abinci ta kwashe tsahon kwanaki 10 tana rashin lafiya ba tare da ta je asibiti ko ta sanar da hukumomin daya dace ba. Mutuwar matar dai ta haifar da fargabar sake barkewar cutar ta Ebola bayan da mahukuntan kasar ke tsallen murnar cewa ta zamo tarihi.