Ebola ta ɓulla kuma a wani yankin na Guinea | Labarai | DW | 03.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola ta ɓulla kuma a wani yankin na Guinea

Gwamnatin Guinea ta ce ta gano wasu ƙarin mutane da suka kamu da cutar Ebola a wani yankin ƙasar da cutar ba ta kai ba tun can da farko.

Wani babban jami'in kiwon lafiya da ke jagorancin kwamitin gaggawa da ke yaƙi da cutar ta Ebola a Guinea. Abubakar Sidiki Diakite ya ce an gano waɗanda ke ɗauke da ƙwayoyin cutar mutane guda tara a garin Damaro da ke cikin lardin Kerouane da ke a yankin kudu maso gabashi na ƙasar.

Ofishin ministan kiwon lafiya na ƙasar ya ce mutane 18 aka sakawa ido ana lura da su a yankin bayan da wani ɗan ƙasar Laberiya da ke fama da cutar ta Ebola ya shigo garin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman