Ebola ta ɓulla kuma a wani yankin na Guinea
September 3, 2014Talla
Wani babban jami'in kiwon lafiya da ke jagorancin kwamitin gaggawa da ke yaƙi da cutar ta Ebola a Guinea. Abubakar Sidiki Diakite ya ce an gano waɗanda ke ɗauke da ƙwayoyin cutar mutane guda tara a garin Damaro da ke cikin lardin Kerouane da ke a yankin kudu maso gabashi na ƙasar.
Ofishin ministan kiwon lafiya na ƙasar ya ce mutane 18 aka sakawa ido ana lura da su a yankin bayan da wani ɗan ƙasar Laberiya da ke fama da cutar ta Ebola ya shigo garin.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman