Ebola na kama jarirai a Kwango
November 24, 2018Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ta samu rahoton bullar cutar Ebola a wannan makon a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a tsakanin jarirai.
A cewar hukumar wannan mummunar alama ce ta yadda cutar ke kara yaduwa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar ta Kwango wadda ke fama da rikici.
Wani kiyasi na baya-bayan nan da hukumar ta WHO ta fitar, ya nunar da cewa sun samu rahoton cutar ta Ebola a jikin jarirai da kuma kananan yara 'yan kasa da shekaru biyu.
Haka nan ma ta samu rahoton kamuwa da cutar a tsakanin yara shida da shekarunsu suka kama daga biyu zuwa 17, yayin da aka samu wata mata mai dauke da juna biyu da ke dauke da cutar.
Kwararru dai sun yi amannar cewa yaran na kamuwa da cutar ne ta hanyar shayar da su nonon uwa.
Matsalar na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar ta lafiya ta duniya ta kaddamar da sabon yaki da cutar ta Ebola, a dai-dai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a yankunan Kivu da Ituru da ke fama da bala'in Ebolan.