1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola da tsaron Nijar sun dau hankalin jaridun Jamus

Usman Shehu Usman AS
October 19, 2018

Cutar Ebola da ta sake bulla a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango da kokari da ake yi na tallafawa Nijar ta fuskar tsaro da 'yan gudun hijira sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/36qhh
Demokratische Republik Kongo | Ebola
Hoto: Getty Images/J. Wessels

Jaridar Die Welt a wannan makon ta rubutar sharhinta kan snnobar cutar Ebola a Jamhuriyar demokradiyar Kongo inda ta hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta bayyana cewa in har ba a dau matakin gaske ba cutar na iya zama barazana ga yankin gabashin Afirka baki daya, sai dai yanzu ana fatan ganin cewar cutar ba za ta kai ga tsallakawa ga kasashe makobta ba bisa matakan gaggaawa da aka dauka na samar da magunan riga kafin.

Ita kuwa jaridar der Freitag a nata sharhin cewa ta yi za a tura jami'an tsaro na kasashen Turai zuwa kasashen Afirka. Jaridar ta leka Jamhuriyar Nijar ne kan wannan batu inda ta ke cewar kasashen Tarayyar Turai na shirin kafa sansanin tsugunar da 'yan gudun hijira da ke son shiga Turai ta barauniyar hanya. A cewar jaridar, matalauciyar kasa kamar Nijar na bukatar tallafi kan wannan batu. 

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta nata sharhin ne kan 'yancin jama'a da aka fara samu a kasar Eritiriya. To sai dai jaridar ta aza tambaya, inda ta ce wannan sauyin da ake samu daga Asmara wai gaba dayan nufinsa kan a bai wa kasar ceto ne ko kuma so take ta jawo hankalin masu zuba jari?  Sannu a hankalin kasar da ake yi wa mulkin kama karya, hukumomi sun fara dan sassauta wa jama'a, wata kila bisa sauyin da ake samu daga makobciyarsu kasar Habasha. 

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ita kuwa cewa ta yi an samu matukar ci gaba wajen tsarin bada tazarar haihuwa a duniya. Jaridar na sharhi ne bisa rahoton hukumar kula da karuwar al'umma ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNFP wacce a rahoton da ta fitar wannan mako ta bayanan cewa a fadin duniya yanzu mata da dama na daukar matakin bada tazarar haihuwa.